Jagora

Cikakken bayani game da yadda ake ƙirƙirar akawun a manhajar GitHub, da kuma yadda ake ɗora portfolio, har ma da yadda ake hosting/deploying.

Buɗe Akawun A GitHub

Idan baku da akawun a GitHub, abu na farko da za kuyi shine ku buɗe ta hanyar amfani da wayar ku ta hannu. Ku sani kyauta ne buɗe wa.

  1. Zaku shiga browser (kamar Chrome ko Safari) sannan ku tafi zuwa ga github.com/signup.
  2. Bayan kun shiga, zaku tarar da fam wanda zaku cike.
  3. Zaku saka adireshin imel ɗinku (ku tabbatar yana aiki).
  4. Zaku saka kalmar sirri.
  5. Zaku saka username, yana da muhimmanci ku zaɓi wanda kuke so (misali: fatima-cs ko sunusi-kano).
  6. Sai ku danna madanni a can ƙasa da aka rubuta "Create account".
  7. GitHub zasu tura muku lambobin sirri na musamman (OTP) zuwa imel ɗinku.
  8. Zaku shiga imel ɗinku ku kwafo wannan lambobi, sai ku dawo cikin browser ku rubuta su.
  9. Sannan sai ku danna madannin da aka rubuta "Continue".

Ƙirƙirar Repository A GitHub

Bayan kun buɗe akawun a GitHub, mataki na gaba shine ƙirƙirar repository.

  1. Zaku shiga browser (kamar Chrome ko Safari) sannan ku tafi zuwa ga github.com/new.
  2. Bayan kun shiga, zaku tarar da fam wanda zaku cike.
  3. Zaku duba akwatin da aka rubuta "Repository name", sai ku saka username ɗinku na GitHub tare da ".github.io" da ƙananan haruffa (misali: idan username ɗinku shine "aminu-kano", sai ku saka "aminu-kano.github.io").
  4. Sai ku tsallake duk sauran akwatinan, ba dole sai kun cike su ba.
  5. Sannan sai ku danna madannin da aka rubuta "Create repository".

Ɗora Portfolio A GitHub

Bayan kun ƙirƙiri repository ɗin ku, mataki na ƙarshe shine ku fitar da shafukan ku daga cikin ZIP file ɗin da kuka yi dan-lodin, sannan ku ɗora su a cikin GitHub.
Idan kuma baku yi dan-lodin ɗin portfolio ba to ku koma zuwa nan kuyi dan-lodin tukuna.

  1. Ku shiga cikin "Files Manager" ko "Downloads" na wayarku.
  2. Ku nemo file ɗin da kuka sauke mai suna "Portfolio_sunanka.zip".
  3. Ku danna file ɗin sannan ku zaɓi "Extract" ko "Uncompress". Wannan zai fitar muku da ainihin shafukan ku (su index.html, about.html, da hotonku na profile.jpg).
  4. Bayan kun gama "Extract", ku koma cikin browser ɗinku inda kuka ƙirƙiri repository ɗin.
  5. A tsakiyar shafin, zaku ga wani rubutu mai shuɗi wanda aka rubuta "uploading an existing file", ku danna shi.
  6. Sai ku danna "Choose your files". Wayarku zata buɗe muku inda zaku zaɓi fayilolin ku.
  7. Ku shiga cikin folder ɗin da kuka yi "Extract" ɗazu, ku zaɓi DUKKAN shafukan gaba ɗaya (ku haɗa da hotonku na profile.jpg).
  8. Sai ku jira har sai sun gama ɗoruwa, sannan ku tafi can ƙasa ku danna koren madanni mai suna "Commit changes".

Ganin Shafin Ku A Yanar Gizo

Bayan kun danna madannin commit changes, kun ci ƙarfin aikin. Shafin ku zai hau yanar gizo kai tsaye.

  1. Ku ba shi kamar minti biyu zuwa uku domin GitHub su gama tsara komai.
  2. Ku buɗe sabon tab a browser ɗinku sannan ku rubuta ainihin sunan repository ɗin da kuka ƙirƙira dazu. Wato username ɗinku tare da ".github.io" a gaba.
  3. Misali idan username ɗinku shine "aminu-kano", sai ku rubuta "aminu-kano.github.io" a browser.
Shuaib Yusuf Shuaib

Hi, I am Shuaib and the developer behind Faka-Faka.
I built this tool to help our department launch clean and professional portfolios instantly.

Check out my portfolio and my GitHub